An Sare Hannun Wani Makiyayi A Kudancin kaduna 


Wasu matasa  dauke da makamai sun sarewa wani makiyayi hannu a yankin kudancin Kaduna. 

Haruna Tugga shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Kaduna, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai. 

Ya bayyana harin a matsayin wani cibaya a yunkurin da ake na samar da zaman lafiya a yankin.

  Tugga ya bayyana mutumin da abin yafaru akansa mai suna Abubakar Muhammad wanda yace yana hijira  ne daga kauyen  Panda a karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa, zuwa Kachia dake kudancin Kaduna lokacin da aka kai masa harin. 

“Abubakar Muhammad wanda yake tafiya daga kauyen Panda, karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa zuwa Ladduga, a karamar Kachia dake jihar kaduna wasu matasa daga kauyen Maho a yankin Mazuga sun kai masa hari. 

“Sun kai masa hari a kan burtalin  da aka ware domin bin dabbobi saboda wani dalili da su kadai suka sani, suka cire masa hannun hagu suka barshi cikin jini.

“Wani mutumin kirki ne yakaishi wani asibiti  mai zaman kansa a garin Kachia inda yake samun kulawar likitoci. ”

Tugga yayi kira ga jami’an tsaro da su binciki lamarin domin ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin.  


Like it? Share with your friends!

0

You may also like