An Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ta Saki Sambo Dasuki An shawarci gwamnatin tarayya da ta saki tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Sambo Dasuki kana ta saka ido akansa idan ana tunanin zai zama barazana. 

A wata sanarwa da aka fitar a Abuja, wani masani kan harkar tsaro kuma jigo a jam’iyar APC, Cif Jackson Lekan Ojo,yace cigaba da tsare Dasuki ya saba ka’ida, ana kuma ganin haka a matsayin wata bita da kullin siyasa. 

Cif Ojo,  wanda shine jami’in tsare-tsare na kasa a kungiyar Yoruba Youth Alliance yace dole ne kowa ya goyi bayan yaki da cin hanci amma ya shawarci gwamnatin tarayya kada ta maida kanta abar dariya.

“Wannan Yariman dan gidan sarautar daular Sokoto, babu wata Kotu da ta aiyana shi da laifin cin amanar kasa, da har zai sa a tsare shi  lokaci  mai tsawo.Yakamata a bada belinsa koda da wasu ka’idoji ne. Har yanzu babu wata kotu da ta same shi da laifi.

” Ina kuma so na bada shawarar cewa a sake shi,  sannan a saka masa matakan tsaro   idan ana ganin zai iya zama barazana ga harkar tsaron kasa, ” yace.
 

You may also like