An Shawo Kan Yaduwar Cutar Ebola A Kasar Jamhuriyar Dimokwaradiyar Kongo  Jamhuriyar Dimokwaradiyar Kongo bata samu sabon rahoton bullar cutar Ebola ba cikin kwanaki 21, Mafi yawan da cutar take dauka kafin ta bayyana a jikin mutum. 

Ministan lafiyar kasar ya bayyana haka a yau Juma’a. 

” A wannan mataki muna iya cewa an kawo karshen yaduwar cutar, godiya ga kwararru ma’aikata na gida da kuma kasashen waje da aka tura zuwa yankin na cutar ta bulls, ” Oly Kalanga ya fadawa manema labarai a Kinshasa babban birnin kasar.

Kalanga  yace hukumomi sun tabbatar da cutar akan mutane hudu karin mutane biyu da aka samu tun da fari, kana  mutane uku meyuwa suna dauke da cutar. 

Mutane hudu ne suka mutu daga ranar 1 ga watan Mayu da aka bayyana barkewar cutar a wani yanki dake iyakar kasar da Jamhuriyar Afirika ta Tsakiya.

Hukumomin lafiya sun amince da ayi amfani da sabon maganin   rigakafin cutar dake matakin gwaji.

 Wannan ne dai karo na takwas da cutar take barkewa a kasar wanda hakan yasa kasar ta zama ta farko a duniya da cutar tafi yawan barkewa. 

An dai gano cutar ne a shekarar 1976 a wani daji mai sarkakiyar gaske dake kasar ta Kongo inda aka bata sunan wani kogi ‘Ebola’dake kusa da inda aka gano kwayar cutar.  


Like it? Share with your friends!

0

You may also like