A Karamar Hukumar Danbatta Dake Jihar Kano, Sarkin Ban Kano Hakimin Danbatta Alhaji Dr. Muktar Adnan Ya Kaddamar Da Dokokin Aure A Fadar Shi Dake Garin Na Danbatta A Aranar 2/1/2017 Wanda Mataimakin Shugaban Kwamitin Alh Ado Muhammed Ya Karanta Kamar Haka:
Mutanen Danbatta A bisa Jagorancin Sarkin Ban Kano Hakimin Danbatta Alhaji Dr. Muktar Adnan, Shugaban Karamar Hukumar Danbatta, Magadai, Masu Unguwanni, Dattawa Da Sauran Matasa Maza Da Mata Sun yarda Sun Amince Da Kudin Dokokin Aure Kamar Haka Don Rage Yawan Al’adun Wajen Yin Aure.
KASHI NA 1 KUNDIN AURE /BAIKO.
1. Daga Dubu Goma Zuwa Ashirin.
2. Mutum Biyu Za a Aiko Yayin Sa Baiko.
3. Bayan An biya Kuma Iyayen Budurwa Sun Amince, Ba a yarda A Kara Dora Wata Hidima Akan Angina.
4. Ba Yarda Wani Ya Nemi Budurwar Da Akaiwa Baiko Ba.
5. Idan Aka Kama Wani Ya Karya Wannan Doka Za Hukunta Shi Ta Hanyar Zama Gidan Maza Ko Biyan Tarar Kudi Adadin Kudin Baiko A gaban Kuliya.