An soki shafin sada zumunta da muhawara na Facebook saboda wuce gona da iri na goge daya daga cikin fitattun hotunan yakin Vietnam da ya nuna wata yarinya tsirara tana tserewa harin Napalm.
Jaridar kasar Norway mai suna Aftenposten, ya ce kamfanin na takaita ‘yancin saboda rashin tantance wa tsakanin hotunan batsa na kananan yara da kuma hotonan tarihi.
Jaridar ya yi amfani da hoton yarinyar domin bayyana matakin da Facebook ya dauka na dakatar da shafin wani mawallafi dan kasar ta Norway har na tsawon wasu makwanni saboda ya yi amfani da hoton.
Shi ma Firai Ministan kasar Norway wanda ya yi amfani da hoton domin nuna adawa daga bisani tilas ya cire daga shafin sa.