An Soma Tantance Wadanda Za Su Amfana Da Tallafin Naira Dubu Biyar A Jihar BauchiGwamnatin jihar Bauchi ta soma aikin tattance wadanda da za su ci moriyar shirin bada tallafin naira dubu biyar ga marasa karfi da matasa a duk wata. Inda ta soma aikin tantacewar da na’urorin tattacewa na zamani. 
A wata takardar sanarwa daga ofishin mataimakin gwamnan Bauchi na musamman kan Sadarwa Malam Shamsudeen Lukman Abubakar, ta rawaito an bayyana cewa a yanzun haka masu tattacewa sun kammala aiki a kananan hukumomin shida, inda nan ba da dadewa ba, za a kammala a sauran kananan hukumomin da suka rage. 
Yanzu haka mabukata kimanin 10,800 suka ui rijista, inda aka bukaci wadanda za su ci moriyar shirin da su kasance a unguwanninsu ko mazauninsu don ganin an tattace su.

You may also like