A safiyar yau ne mabiya Shi’a suka fito domin gudanar da Muzahara amma hakan su bai cimma ruwa ba inda suka sha barkono mai sa hawaye.
Haka makamancin haka ya auku a yanzu haka a masallacin Fagge dake cikin birnin Kano, inda jami’an sanda suka dinga har barkonon tsohuwa sama.
Sai dai babu tabbacin ko akwai wadanda suka ji rauni ko suka rasa ransu.
Idan baku manta ba a ‘yan kwanakin nan ne yan Shi’a sun samu kalubale daga wasu jahohi har kamar Kaduna, Kano da Katsina.