Amurka kuma ta gargadi Amurkawa da su yi hattara saboda akwai yiwuwar kai hare-hare kan wasu hotel-hotel dake Lagos a lokacin bukukuwan sallah gobe da jibi
Kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sani Kukasheka Usman, ya ce sojoji sun harbe matan suka kashe su kafin su tayar da bama-baman dake jikinsu a kusa da wani sansanin ‘yan gudun hijira.
Wasu daga cikin bama-bama dake jikin maharan sun tashi bayan da aka harbe su.
Fararen hula biyu sun ji rauni a wannan lamarin da ya faru a bayan garin Monguno dake Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda kungiyar ta Boko Haram ta yi tunga.
Sanarwar ta ce wata ‘yar kunar-bakin-wake ta tayar da nata bam din ta kashe kanta a wani wuri. Babu wanda ya ji rauni daga ta ukun.
A halin da ake ciki, Amurka ta yi gargadi yau talata game da yiwuwar kai hare-hare a kan ‘yan kasashen waje a cibiyar kasuwanci ta Najeriya, lagos a lokacin bukukuwan Sallar azumin nan.
Wata sanarwar da aka buga a shafin intanet na ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, tace kungiyoyi masu alaka da ayyukan ta’addanci suna shirya kai hare-hare a kan hotel hotel inda baki ‘yan kasashen waje suka fi zuwa a Lagos, ciki har da wadanda ke bakin ruwa.
Gargadin bai ambaci sunan wata takamammiyar kungiya ba, amma kuma ya bukaci Amurkawa da su sanya idanu sosai kan abubuwan dake faruwa a kusa da su, su kuma rika kasa kunnuwa ga kafofin labarai na inda suke.