An tilata wa ‘ya’yanmu bayar da fasfo ɗinsu kan a kai su Masar – Iyayen ɗaliban Sudan



G

Hausawa kan ce tsuguno ba ta ƙare ba a kan lamarin ɗaliban Najeriya da ke karatu a Sudan, waɗanda gwamnatin Najeriyar ta ce za ta kwaso su zuwa gida.

Yayin da ake kukan cewa har yanzu akwai tarin ɗalibai da aka bari a ƙasa – a gefe ɗaya kuma iyayensu na kukan lokaci na ƙurewa, ko da yake an tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙarin sa’a 72.

Iyayen ɗalibai da dama da BBC ta tattauna da su, sun ce yanzu haka halin da yaransu ke ciki ya fi wanda suka baro a Khartoum.

Asma’u Yarima Muhammad, sakatariyar ƙungiyar iyayen ɗaliban Najeriya da ke karatu a Sudan, ta ce ‘ya’yanta biyu “na cikin tsakiyar sahara ba tare da sanin inda suka dosa ba”.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like