Yadda na tarar da gaskiyar labarin manya manyan tukwanen da aka tono a unguwar zangon barebari dake tsohon Birnin kano…
Mai Unguwa Mal Auwal Rabiu ya shaida mun cewa tun bayan da aka hako wadannan tukwane a unguwarsa mutane suke zuwa daga dukkan unguwannin jihar Kano don kallon tukwanen. Sannan ya cigaba da cewa zuwa yanzu ba a samu damar bude tukwanen ba, saboda jami’an gwamnantin tarayya masu kula da kayan tarihi sun zo sun duba tukwanen inda suka ce kada a bude har sai sun zo da kayayyakin aiki sannan a bude tukwanen kuma a daukesu zuwa museum wajen adana kayan tarihi…..
Da na tambaye shi akan gwala-gwalan da ake tunani akwai a ciki, sai ya ce shi ma yana zargin akwai tarin dukiya a ciki amma dai babu wanda ya bude ballantana a san abun dake ciki, sannan sun dauki matakan tsaron bawa tukwanen kariya har zuwa lokacin da zaa bude tukwanen…..
Tukwanen guda uku ne kuma sun bayyana ne a wani bangare na gidan da yake da babban tarihi a unguwar.
Alhaji Turaki shine wanda ake yi wa aiki a wajen sannan iyalan gidan suna nan yanzu haka inda suke cigaba da mu’amularsu a ragowar bangaren gidan.
Wajen ya zama wajen yawon bude idanu saboda tururuwar da akeyi zuwa kallon wadannan tukwanen da baa saba ganin irinsu ba….
Dana tambaye shi ko zai iya fadar adadin shekarun tukwanen, sai yace bazai iya sani ba amma dai ga dukkan alamu sun shige shekara dari a wajen tunda unguwar tsohuwa ce wqcce kakanninsa suke mulkinta tun sama da shekara dari da hamsim… yace su jamian gwamnantin da suka zo sun sanar dashi zasuzo da kayan aikin da zasu bincika adadin yawan shekarun tukwanen……