An tsare wani mutum a gidan yari kan laifin yiwa mara lafiya fyade


Wata kotun majistire dake zamanta a Nomans Land a Kano ta bada umarnin tsare wani kantin siyar da magani a gidan yari  kan zargin yi wa wata mara lafiya fyade.

Mazaunin kauyen Kafin Agur a karamar hukumar Madobi, Danjummai mai shekaru 45 ana zarginsa da aikata laifukan biyu da suka hada da aikata sojan gona da kuma laifin dukan laifukan biyu sun saba da sashi na 283 da kuma na 132 kundin shari’ar penal code.

Mijin matar, Sagiru Buhari wanda ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin yan sanda na Madobi yace Danjummai ya yiwa  matarsa fyade a yadda takardun karar suka nuna.

 Takardun tuhumar da akewa Isa sun nuna cewa ya hilaci matar lokacin da taje shagonsa neman magani.

” Mutumin da ake zargi ya kwanta da  matar aure mara lafiya lokacin da yake kokarin yi mata magani,” a cewar takardar karar.

Takardar ta kara da cewa matar taji haushi sosai kuma ta kadu matuka da abin da yafaru saboda haka ta sanar da mijinta.

Yayin da ake gudanar da bincike an gano cewa Danjummai  ba ma’aikacin lafiya ne ba.

Alkalin kotun mai shari’a, Maryam Ahmad,ta bada umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yari ta kuma daga karar zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like