An tsaurara matakan tsaro a Damaturu gabanin ziyarar shugaban kasa Buhari


Hoton sojojin Najeriya

An tsaurara matakan tsaro a Damaturu da kewaye gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammad Buhari zai kai jihar Yobe da safiyar yau.

Jaridar Daily Trust ta lura cewa an jibge jami’an tsaro a wasu muhimman wurare ya yin da wasu suke gudanar da sintiri a titunan garin cikin motocin Hilux da kuma na silke.

An rufe wasu tituna da kuma manyan hanyoyi dake da yawan hada-hadar mutane musamman titin zuwa Maiduguri inda jirgin shugaban kasar zai sauka haka ma shaguna dake sayar da kaya akan titin duk an rufe su.

Malam Yusuf Balube wani dan siyasa ya koka cewa hana mutane su yi wa shugaban kasar zai yi illa ga farin jinin shugaban kasar a siyasance.

You may also like