An tsaurara tsaro a New York


Gwamnan New York a Amurka, Andrew Cuomo, ya ce za a tura da karin ‘yan sanda da jami’an tsaron kasa na National Guard 1,000 sassa daban-daban na birnin a wani mataki na kan-da-garki, bayan harin ranar Asabar wanda ya raunata mutum 29.
Ya kwatanta harin da cewa wani aiki ne na ta’addanci, amma babu wata hujja dake alakanta shi da ‘yan ta’adda na duniya.

Ya kuma yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifin dasa bam din, da ma wani abun fashewa da bai tashi ba wanda aka samu a kusa da wurin.

Zuwa yanzu dai an sallami dukkan mutanen da suka yi rauni su 29 daga asibiti.

You may also like