An Tsige Kakakin Majalisar Jihar Edo Majalisar Dokokin jihar Edo a Najeriya ta tsige shugaban majalisar jihar Mista Justin Okonoboh, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
A ranar Litinin ne aka tumbuke Mista Justin yayin wani zama a zauren majalisar da ke birnin Benin City.

Sai dai jagoran majalisar ya ce cirewar da aka yi masa ta saba wa doka, kuma har ma ya ba da umarnin dakatar da ‘yan majalisar da suka tsige shi.

You may also like