An tsinci Gawar Wani Yaro Wanda Akayi Garkuwa Da Shi A Kano


Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Dabai inda aka ga gawar yaran mai suna Usman Dan shekaru shida. Inda aka kwana biyar ana nemansa amma bisa kokarin jami’an tsaran DSS suka gano wanda ake zargi mai suna Abubakar Maikudi. Wanda kuma wa ne ga mijin yayar marigayin ne.

Tuni dai an cafke wadanda ake zargi da aikata wannan danyan aikin.

Tunda fari dai an dauke yaron ne bayan taso su daga makaranta, daga bisani suka nemi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa, shi kuma yaron ya gane yayan mijin yarsa shine sanadin kashe shi kamar yadda ake zargi.

You may also like