An tuhumi Man United da Palace da kasa tsawatarwa juna



Man United Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Manchester United da Crystal Palace da tada jijiyar wuya a Old Trafford ranar Asabar a Premier League.

Lamarin ya faru, bayan jan katin da aka yi wa dan wasan United, Casemiro, sakamkon shakar wuyan Will Hughes da ya yi.

An tuhumi kungiyoyin biyu da kasa tsawatarwa ‘yan wasansu a karawar ta babbar gasar tamaula ta Ingila.

FA ta ce ”United ta kasa hana ‘yan wasanta yin halayyar da za ta iya tayar da yamutsi” a karawar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like