
Asalin hoton, OTHER
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi dan wasan gaban Brenford Ivan Toney, da keta dokokin caca guda 30.
A watan da ya gabata ne aka zargi dan wasan da keta dokokin cacar sau 232.
Toney ya ci kwallaye 10 a gasar Premier League kawo yanzu, to amma duk da haka bai samu shiga tawagar Ingila ba, da ta je gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar.
A sanarwar da kungiyarsa Brentford ta fitar, ta ce ” Muna kan tattaunawa da Ivan da lauyoyinsa. Za mu cigaba da tattaunawar cikin sirri.”
Sanarwar ta kara da cewa ” Ba za mu sake cewa komai ba har sai mun kai karshen tattaunawa.”
Toney na da daga nan zuwa 4 ga watan Janairu ya yi wa hukumar ta FA bayani, wadda ta hana yan wasa cacar wasanni, ko kuma bada bayani game wasa ga masu caca.
Idan har aka kama Toney da laifi, to kuwa zai fuskanci dakatarwa ta tsawon lokaci.
A 2020 an taba dakatar da dan wasan Newcastle da Ingila Kieran Trippier makonni 10, saboda bai wa wasu mutane bayanai suka shiga cacar komawarsa Atletico daga Tottenham.
Ko a 2017 an dakatar da Joey Barton watanni 18, bayan amsa laiifn cacar wasanni.
A hira da manema labarai farkon watan nan, Toney ya ce zai bai wa hukumar FA hadin kai wurin gudanar da bincike.