An Tura Ni Kai Harin Kunar Bakin Wake Saboda Nace Bazan Auri Dan BokoHaram Ba Wata ‘yar shekara 14 da aka kama a Maiduguri dauke da bama bamai a jikinta ta bayyana cewa an tura ta kai harin kunar bakin wake ne bayan da taki amincewa ta auri daya daga cikin mayakan Boko Haram.

Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya ya ruwaito yarinyar tana cewa a shekarar 2013 ‘yan Boko Haram suka kama ta ita da mahaifinta a lokacin da suke kokarin tserewa daga Gwoza inda ta nuna cewa  mutune uku daga ‘yan kungiyar Boko Haram din sun nuna sha’awar aurenta amma ta jaddadawa mahaifinta cewa gara ta mutu a kan ta aure daga cikinsu.

A cewarta, a kan haka ne, suka yanke shawarar tura ta garin Maiduguri don kai harin kunar bakin wake inda aka hada su da wani namiji daga Dajin Sambisa zuwa garin Maiduguri inda a nan ne aka dora masu abubuwan fashewa a jiki su uku mata amma ita ta ki tayar da nata Bom din.

You may also like