An Turani Kai Harin Kunar Bakin Wake Saboda Naki Yarda Na Auri Kwamandan Boko Haram, A Cewar Wata Yarinya 



Wata mace da ake zargin ta da yunkurin kai harin kunar bakin wake,tace an zabeta ne takai harin kunar bakin waken sakamakon kin amimcewa da tayi ta auri kwamandodin Boko Haram har karo uku.

Yarinyar yar shekara 14, tace shugaban nin Boko Haram ne suka zabeta tare da wasu mutane biyu domin su kawo harin kunar bakin wake a birnin Maiduguri.

Sojoji ne suka tsare ta tare da mutanen   uku lokacin da take yunkurin kai hari a Jankana, Maiduguri. 

Wacce ake zargin tace ita da mahaifinta ,Usman,  suna gudu zuwa tsaunukan mandara domin tsira da rayukansu lokacin da yan kungiyar suka sace su a Gwoza,jihar Borno a shekarar 2013.

” Na shafe shekaru uku a hannun Boko Haram, yan ta’addar su uku sun nemi su aure ni amma naki.” tace

“Lokacin da naki yarda a karo na uku daya daga cikin kwamandodin ya fusata inda yayi barazanar kashe ni tare da mahaifina na fada masa gara na mutu dana auri dan Boko Haram .

” To bayan sati daya sai su kace tunda naki yadda nayi aure to za a turoni kunar bakin wake Maiduguri, mutane uku daga ciki suka rike hannuna inda suka yimin allura.

” Daganan ban san abinda yake faruwa ba. 

“An dauke ni zuwa wurin mai magani, bayan na farfado yace min kwanana 30, ina tare dashi. 

“Yace yana shiryani domin kai hari inda yabani wani ruwa nasha ban san ko meye ba amma nasha inda yace yau zasu zo su dauke ni. 

“Da misalin karfe 7 na dare yan kungiyar su uku,suka zo tare da wasu mutane biyu namiji da mace suma an daukesu sukai hari ne kamar ni. 

” Mun shafe kwana daya da rabi muna tafiya kafin mu iso Maiduguri, inda suka daura mana rigar bom a wannan lokaci nasan mutuwa zanyi  kawai sai nafara kuka.

“Ina kallo mace ta farko ta tayar da bom din da yake jikinta a kusa da wurin bincike na sojoji inda ta kashe kanta ita kadai, shi kuma namijin aka harbeshi kafin ya tayar da bom din.

”  A wannan lokacin kawai naji yakamata na cire rigar bom din,na kuma mika wuya ga jami’an tsaro haka kuwa akayi,sojoji suka zagayeni daga anan na fadi na suma. 

“Lokacin dana farfado ,sai naga ashe dan sandan da yake tsaye a kaina kanin mahaifiyata ne, ina ganin dalilin da yasa na rayu kenan.” 

You may also like