An ya Liverpool za ta shiga ‘yan hudun Premier kuwa?



Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta tashi 0-0 da Chelsea a kwantan wasan mako na takwas a gasar Premier League da suka ranar Talata a Stamford Bridge.

A wasan farko ma a Janairu haka suka tashi, sau hudu a jere suna raba maki a tsakaninsu a dukkan fafatawa

Karo na uku da manyan kungiyoyin Premier na raba maki a fafatawa hudu a jere, bayan Everton da Liverpool tsakanin 1974 – 1975 da na Arsenal da QPR tsakanin 1992 – 1994.

Da wannan sakamakon Liverpool tana ta takwas a teburin Premier da maki 43, saura wasa 10 ta kammala fafatawar bana.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like