An Yabawa Gwamnan Bauchi Bisa Gudanar Da Sahihin Zaɓen Shugabannin APC A Jihar


An yabawa Gwamnan Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar game da zaben shugabannin gunduma na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Bauchi a makon da ya gabata.

Gamayyar Kungiyoyin sa kai na Nijeriya wato ‘The Coalition of Civil Society Organizations in Nigeria’, ita ta yabawa Gwamnan game da zaben, inda ta bayyana zaben a matsayin babbar nasara ga siyasar Nijeriya.

Baya ga yabawa Gwamnan a yayin taron manema labarai, gamayyar kungiyar ta kuma yabawa al’ummar jihar Bauchi game da zaben wanda ya hada kan ‘yan takarar. Haka kuma sun yabawa jami’an tsaron da suka yi sintiri a wuraren zabukan daban-daban.

Takardar yabon wanda ke dauke da sa hannun ko’odinetan kungiyar, Michael Babatunde, ta kara da cewa, bayan rahotannin da suka fito game da zaben, sun samu bayanin cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a sassa daban-daban na fadin jihar wanda aka gudanar a karkashin shugabannin jam’iyyar na ciki da wajen jihar.

Kungiyar ta kara da cewa sakamakon nasarar da aka samu wajen gudanar da zaben, sun yi matukar yabawa da yadda zaben ya gudana. Sannan kuma suna kira ga al’ummar jihar da su kasance sun gudanar da zabe makamancin haka a yayin zaben kananan hukumomi dake tafe.

You may also like