
Asalin hoton, Getty Images
Kotu a Indiya ta yanke wa jagoran ƴan adawa na ƙasar Rahul Gandhi hukuncin ɗauri na shekara biyu bayan samun sa da laifin zubar da mutunci.
Wata kotu a jihar Gujarat ce ta kama Gandhi da laifi kan kalaman da ya yi a shekarar 2019 a kan firaminista Narendra Modi, lokacin wani gangami na siyasa.
A yanzu ɗan adawar na da tsawon kwana 30 domin ya ɗaukaka ƙara.
Ɗan adawar wanda ɗan majalisa ne a halin yanzu ya halarci zaman kotun a lokacin da aka yanke hukunci.
Kuma hakan na zuwa ne shekara guda gabanin zaɓen ƙasar na gaba.
Lokacin wani gangamin siyasa a watan Afrilun 2019, gabanin babban zaɓen ƙasar, Mr Gandhi ya ce “Me ya sa duk ɓarayin nan suke sa Modi a sunansu? Nirav Modi, Lalit Modi, Narendra Modi.”
Nirav Modi wani hamshaƙin mai dukiya ne da ya samu kuɗinsa a harkar lu’u lu’u, wanda ya tsere daga ƙasar yayin da shi kuma Lalit Modi tsohon mai ruwa da tsaki ne a gasar firimiyar wasan kurket na ƙasar ta Indiya, wanda hukumar kula da kurket ta ƙasar ta haramta masa samun duk wani shugabanci a cikinta, har abada.
Mr Gandhi ya ce ya yi kalamin ne kawai domin nuna yadda rashawa ta yi kaututu a ƙasar, kuma ba ya yi ne domin cin zarafin wani ba.
Wani ɗan majalisa mai suna Purnesh Modi ne ya shigar da ƙarar, bisa iƙirarin cewa kalaman Mr Gandhi cin mutuncin duk wani mai amsa sunan Modi ne.
Sai dai wasu sun ce lamarin yana da sarƙaƙiya.
Wani masanin shari’a Gautam Bhatia ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa “ba za a iya ɗaukan mataki a madadin wasu gungun mutane da ke amsa wani suna guda ɗaya ba, sai dai idan mutum ɗaya ne.”
“Idan mutum ya ce dukkanin lauyoyi ɓarayi ne, ni a matsayina na lauya ba zan iya shigar da shi ƙara kan ya ɓata min suna ba, sai dai idan na iya tabbatar da cewa da ni yake.”