Rundunar Yansanda Ta Bukaci Da A Yankewa Maryam Sanda Hukuncin Kisa 


Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja ta shigar da kara babban kotun tarayya da ke Abuja tana neman a yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa saboda kashe mijinta Bilyaminu Bello Halliru da tayi. 

Ana zargin Maryam Sanda da dabawa mijinta Bilyaminu fasasshiyar kwalba da niyyar kashe shi, bayan aikata haka Bilyaminu ya rasu sanadiyar sara. 

‘Yan sanda sunce wannan abu ya faru ne a gidansu da ke unguwar Wuse, Zone 2 ba maitama ba kamar yadda ake ta yadawa. 

Ba a tsayar da ranar fara sauraron karar ba, sai dai har yanzu Maryam na tsare a hannun ‘yan sandan.

You may also like