An Yankewa Matashi Hukuncin Kisa A Garin Zaria bisa Kisan Kai. 


Kamfanin Dillancin labaran Nijeriya wato NAN ya ruwaito cewa wata kotu a garin Dogarawa dake karamar hukumar Sabon garin Zariya a jihar Kaduna ta yankewa wani matashi d’an shekaru 25 hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yankewa matashin hukuncin ne sakamakon zarginsa da kashe wani. A inda kotun ta tabbatar da zargin da ake masa.
Matashin mai suna Hassan Adamu, ya kashe wani saurayi ne mai suna Shamsuddeen Adamu a unguwan Tudun Jukun da ke karamar hukumar Zariya.
Kotu ta kama Hassan Adamu da laifin caka ma Shamsuddeen wuka har wuri uku, ciki, baya da kuma hannu wanda ya zama sanadiyyar mutuwarsa. Alkalin kotun, Kabir Dabo ya yanke masa hukuncin ne bayan an samu matashin da aikata laifin, kuma shima ya tabbatar da hakan.
Sai dai kotun ta sallami dayan matashin da ake zargi da kisan, Abubakar Adamu bayan kotun bata sami kwakkwaran hujjojin yanke masa hukunci ba.
An shigar da ‘karar ne tun shekaru 4 da suka gabata. Wanda Aku Alexander Amadi a madadin gwamnatin Jihar ta shigar.

You may also like