An Yankewa Wata Tsohuwa Mai Shekaru 60 Hukuncin Wata 6 A Gidan Yari Kan Laifin Sata


Hoto: Daily Trust

Wata kotun majistire dake Ikorodu a Jihar Lagos, a yau Litinin ta yankewa wata mata,Adegunwa Adejoke mai shekaru 60 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bayan da ta sameta da laifin fasa wani shago da kuma yinkurin yin sata.

Adejoke wacce ke zaune  a Agbowa-Ikosi a Ikorodu, ta amince da tuhume-tuhume  guda uku da ake mata da suka hada da hada baki, fasa gida da kuma sata.

Alkalin kotun mai shari’a A.B Olagbegi-Adelabu wacce ta yanke hukuncin ta zartar da daurin watanni shida kan kowanne laifi da ake zargin matar da aikatawa.

Amma tace matar zatayi zaman gidan yarin na laifukan a tare. 

Tace ” Bayan yin kalaman amincewa da aikata laifin,wacce ake tuhuma tace wasu mutane ne da suka gudu suka yaudare ta zuwa aikata satar. 

” Amma kuma babu kayan da aka sata a shagon sai dai an sameta da dutsen da tayi amfani wajen balle shagon.

” Saboda haka, ba tare da lura da abinda yafaru ba, ya zama doke kotu ta kare bukatar kasa. 

“An yake miki hukuncin daurin watanni shida kan kowace tuhuma kuma za kiyi zaman hukuncin tare. 

” Wannan zai koya miki darasi ina fata idan kika gama zaman gidan yarin zaki canza hali.”

Tun farko yar sanda mai gabatar da kara Mary Ajiteru,ta fadawa kotun cewa matar da ake zargi tare da wasu mutane da ake nema an kama su ranar 29 ga watan Yuli da misalin karfe 9:00 suna fasa shagon wani mutum mai suna Oladehinde Agbomeji. 

” Mai gadin dake wurin ya kama wacce ake zargi yayin da ragowar mutanen suka ranta ana kare.  

” An kaita wurin basaraken gargajiya na yankin inda yayi umarni da a mikata hannun yan sanda.”

Laifin da ta aikata ya saba da sashi na 305,308 da kuma  409 na kundin dokar manyan laifuka ta jihar Lagos.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like