An Yi Bikin Yaye Daliban Jami’ar Tarayya Ta Birnin Dutsen Jihar Jigawa



Jamiar Tarayya ta Dutse ta gudanar da Bikin yaye dalibai karo na biyu a matsagunin Jami’ar na dindindin wanda Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) ya samu halarta. 
Ɗalibai 290 da suka kammala karatun digiri a fannoni daban daban aka yaye a wajen bikin. 
Daga cikin ɗaliban guda 18 sun sami matsayin first class, sai 131 da suka sami matsayin second class upper, da kuma guda 137 suka sami matsayin second class lower.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin  Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da jami’o’i ta Ƙasa Farfesa  Abubakar Rasheed yace Jami’ar Tarayya ta Dutse na ɗaya daga cikin sabbin jami’o’i tara da aka ƙirƙiro a lokacin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck  Jonathan a Shekarar 2011.
Yace shekaru shida da kafuwar Jami’ar ta yi bikin yaye ɗalibai sau biyu tare da samun nasarori masu tarin yawa.
Ya kuma yaba da haɗin kai da tallafin da mutanen gari da kuma Gwamnatin Jihar Jigawa take baiwa Jami’ar a kowane lokaci.
Yace Gwamnatin Tarayya zata cigaba da tabbatar da ingancin ilmi a jami’o’in ƙasar nan. 
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace an amince da sake tsara Hukumomin Gudanarwa na Kwalejojin Kimiyya da Fasaha da na Ilmi da kuma na Jami’o’i da wa’adin su zai ƙare nan da makonni biyu masu zuwa.
Ya kuma yabawa ma’aikatan Hukumomin masu barin gado tare da baiwa sabbin shugabannin masu zuwa umarnin cigaba da aiyukan da suka tarar maimakon ƙirƙiro sabbin ayyuka. 
Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Hukumar Kula da jami’o’in na Ƙasa da ta ɓullo da sabuwar manhajar ilmi ga Jami’o’i domin ƙara kyautata harkokin koyo da koyarwa. 
Ya kuma shawarci Jami’o’in Ƙasar nan dasu rinƙa gabatar da rahotannisu a duk shekara ta hannun Hukumar Kula da Jami’o’in. 
A jawabinta Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Farfasa Fatima Batul Muktar ta musanta dakatar da karatun aikin likita a Jami’ar, tana mai cewar Jami’ar tana jiran sakamakon aikin tantance kwasa-kwasan na aikin likita ne da aka gudanar a Jami’ar.

You may also like