An yi garkuwa da matafiya fiye da 30 akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.


Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane sama da 30 akan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Lamarin farko ya faru ne ranar Talata da misalin karfe bakwai na dare lokacin da yan bindigar suka tsare wata mota kirar Sharon suka kuma tasa dukkanin fasinjojin dake ciki ya zuwa cikin daji a dai-dai wani gari da ake kira Ladi kusa da Buruku.

Da farkon safiyar ranar Laraba wasu motocin kirar Golf su uku dake tafiya tare saboda yanayin tsaro suma an tsare su aka kuma tasa keyar fasinjojin da kuma direbobin ya zuwa cikin daji.

An ce sai da aka umarci fasinjoji mata da su cire kayan dake jikinsu kafin a shiga dasu dajin.

Shugaban kungiyar yan kamasho ta NURTW reshen Birnin Gwari, Malam Danladi Idon duniya wanda ya tabbatar da sace mutanen ya ce mazauna kauyen ne suka gano kayan matan a cikin mota.

“Watakila sun cirewa matan dake cikin mutanen kayansu kafin su dauke su su yi gaba amma har yanzu babu wanda ya tuntube mu,” ya ce

Idon Duniya ya kara da cewa saboda rashin tsaron dake tattare da hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua babu wata motar haya dake bin hanyar tsawon watanni biyu.

You may also like