An yi garkuwa da matuƙin jirgin sama a Indonesia...

Asalin hoton, AFP

Mayaƙa a yankin Papua na ƙasar Indonesia sun yi garkuwa da wani matuƙin jirgin sama ɗan asalin New Zealand.

An far wa matuƙin, Mr Mehrtens, mai shekara 37 ne bayan da jirginsa mai ɗauke da fasinjoji biyar ya sauka a lardin Nduga mai yawan tsaunuka.

Waɗanda suka sace shi – waɗanda ƴan ƙungiyar TPNPB ne masu ɗauke da makamai – sun shaida wa sashen labaru na BBC Indonesia cewa yana cikin ƙoshin lafiya.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like