An Yi Gobara A Babbar Kasuwar PotiskumA cikin daren jiya Talata, wayewar yau Laraba ne aka tashi da mummunar gobara a cikin babbar Kasuwar Potiskum ta jihar Yobe, wanda aka yi asarar milyoyin nairori. 
Gobarar ta tashi ne a ‘yan Gwanjo da wurin masu sayar da citta da kuma wurin ‘yan kwanuka, inda shaguna sama da 500 suka kone kurmus. Ana zaton cewa kawowar wutar lantarki shine musabbabin tashin wutar, inda ta fara tashi daga shagon wani Tela. 
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar a safiyar yau din nan, ‘yan kasuwar sun nuna bacin ransu sakamakon hana su shigowa su kashe wutar da masu gadin Kasuwar suka yi tun da wuri. Suka ce da an bar su sun shigo sun kashe wutar, da wutar batayi ta’adi haka ba. 
Sannan ‘yan kasuwar suna ta bayyana ra’ayoyin su game da rashin ganin motar kashe gobara ta cikin kasuwar da kuma ta cikin garin Potiskum, suna bayyana cewa “Ina motar kashe gobara ta cikin kasuwar? Me ya hana a kawo ta ta kashe wutar?” Motar kashe gobara daga karamar Hukumar Nangere ne dai tazo ta kashe wutar. 
Sai dai dana tuntubi Shugaban ‘yan Kasuwar Potiskum din ta wayar salula, Alhaji Isah Sakatare ya musanta wadannan zarge zarge da ‘yan Kasuwar suke yi, yace dukkan motocin kashe gobarar an kai su gyara a garin Jos, yace shine yaje ya taho da motar kashe gobara daga Nangere. Ya kara da cewa “An hana shiga kasuwar ne a lokacin da gobarar take ci, saboda barayi, wasu burinsu suyi sata ne ba su kashe wuta ba. Ai ba duka kofofin shiga kasuwar aka hana shigowa ba, an bude kofa uku”

You may also like