An binne Imam Imama, mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, a Abuja bayan an yi masa sallar Jana’iza.
Sallar jana’izar ta gudana a masallacin Annur dake Abuja bayan sallar Juma’a ta samu halartar fitattun yan Najeriya da suka fito daga bangarori na rayuwa daban-daban, yan uwa da kuma abokanan arziki.
An dauki gawartasa ya zuwa makabartar Gudu a Abuja inda aka binne shi.
Cikin wadanda suka halarci jana’izar sun hada da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Abdulmuminu Jibril, Sanata Kabiru Gaya, Shekh Isah Ali Pantami.
Marigayin ya rasu a daren ranar Juma’a wani asibiti dake Abuja bayan yar gajeriyar rashin lafiya.
Ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya hudu.