
Asalin hoton, senate
Sanata Ali Ndume
Wata baraka ta kunno kai a majalisar dattawan Nijeriya inda rahotanni ke cewa an samu wasu sanatoci da ke shirin tsige shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Rahotannin sun ce sanatocin sun nuna rashin jin dadi a kan abinda suka kira kusancin ‘shugaban majalisar da fadar shugaban kasa’.
Sai dai sanata Mohamed Ali Ndume wanda shi ne mai tsawatarwa a majalisar dattawan Nijeriyar ya shaida wa BBC cewa rikicin na da nasaba da korafin da wasu sanatocin su ka yi a kan cewa an nuna mu su wariya wajan rabon mukaman shugabancin kwamitoci da majalisar ta yi a baya baya nan.
Ya kuma amince da cewa an yi kuskure a rabon mukaman amma barakar da aka samu ba sabuwar aba ba ce a cewarsa:
“Akwai ma su guna-guni a kasa amma wannan ba sabon abu bane, bana tsamani ya kai ga cewa lalai lalai ana son a cire shugaban majalisar dattawa, dan bai aikata wani laifi ba da zai kawo ga haka.”
Bayanai sun ce ‘yan majalisar dattawan da galibinsu tun farko ba su goyi bayan kasancewar Akpabio a matsayin shugaban Majalisar dattawan ba, na zarginsa da zama dan amshi shatan fadar shugaban kasa.
Sai dai sanata Ndume ya ce sun fara tattaunawa da bangaren da ke hammaya da nade naden domin samun masalaha:
“ Kamar yadda daya daga cikinsu ya fada , ba a yi mu su yadda aka saba ba dole irin wannan ya janyo ce-ce ku-ce, kuma gaskiya akwai kuskuren da aka yi, saboda akwai tsoffin ‘yan majalisa da ya kamata a ba su shugabancin kwamitoci amma ba a ba su ba.
“ Duk abin aka kawo a gaban majalisar, ai da ‘yan majaisar ne ake yi, kuma ba za a iya cewa ya zama dan amshi shatta na saboda sai da hadin kan ‘yan majalisar dattawa ya ke amincewa da bukatun fadar shugaban kasa .
Sanatan ya ce tuni su ka fara daukar matakin yin gyra ta hanyar tattauna wa da bangaren sanatocin da suke ganin an nuna mu su wariya aa rabon mukaman.