Sojoji da yayan kungiyar Boko Haram sun yi musayar wuta a wani kauye dake karamar hukumar Kada ta jihar Borno.
Wata majiya dake dakarun soja ta fadawa jaridar The Cable cewa yan tada kayar bayan sun farma kauyen akan babura masu kafa uku da kuma motoci dake dauke da manyan bindigogi.
“Yanzu haka da nake magana da kai ana cigaba da gwabza fada.maharan sun kai harin mintuna 15 da suka wuce,” ya ce.
Jaridar The Cable ta gano cewa jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin.
Harin na zuwa ne mako guda bayan da yan ta’addar suka yi yunkurin mamaye birnin Maiduguri amma gamayyar jami’an tsaro da suka hada da sojojin sama da na kasa da kuma yan sanda suka samu nasarar fatattakarsu.
Hari irin wannan na nuna cewa har yanzu kungiyar Boko Haram tana da karfi sosai duk da ikirarin da gwamnati ta keyi na cewa ta murkushe kungiyar.