An Yi Nasarar Yi Wa Yaro Mai Juyayyen kai Aiki


 

Mahendra Ahirwar mai shekaru 13 wanda dan asalin kasar Indiya ne, yanzu haka yakan taka har ma ya yi tafiya sabanin kafin a yi masa aikin. Ko abinci ma sai an tallafa masa kafin ya ci.

Saboda tsananin rayuwar da yake fuskanta har sai da ta kai iyayensa sun gwammace ya mutu.

Wata ‘yar kasar Ingila ce mai suna Julie Jones, ta dauki nauyin neman gudummawar da aka yi masa aikin bayan ta ci karo da hotunan halin da yaron yake ciki. Sannan kuma ta dauki alwashin ci gaba da kawo masa ziyara domin duba lafiyar har zuwa nan da watanni uku.

An kashe kimanin fam dubu 12 na kasar Burtaniya ne wajen yi masa tiyatar.

You may also like