
Asalin hoton, Getty Images
An bai wa tsohon dan kwallon Juventus, Cristian Bunino jan kati, bayan da ya yi fitsari a gefen fili a lokacin da za a saka shi a wasa a Serie C a kungiyarsa Lecco.
Ana shirin saka shi a karawar a minti na 76 a fafatawar rukunin farko a Piacenza, sai fitsari ya kamashi, shi kuwa ya yi abinsa.
Wani daga cikin masu kula da wasan ne ya ga dan kwallon mai shekara 26 na fitsari a gefen fili, shi kuma ya sanar da alkalin wasa, wanda nan take ya bashi jan kati.
Kociyan Lecco, Luciano Foschi ya ce hukuncin da aka dauka kan tsohon dan wasan tawagar Italiya ‘yan kasa da shekara 19 ya yi tsauri.
”Wannan doka ce da ya kamata a zartar, amma na dauka alkalan za su yi amfani da tunaninsu, domin bai yiwa kowa laifi ba, kuma ba wanda ya ganshi,” kamar yadda Foschi ya sanar da Gazzetta dello Sport.
”Na yi fatan za a bashi katin gargadi, amma alkalin wasa bai yi kuskure ba, shi kansa Bunino a hange na, bai san hukuncin da za a yi masa ba.”