An Yi Wa Wata Tsohuwa Yankan Rago A Kaduna



Da Yammacin jiya Talata ne wasu da ake zargin barayi ne suka aika da wata tsohuwa lahira ta hanyar yankadta da wuka a yankin G.G dake unguwar Dosa a Kaduna.
An bayyana cewar barayin sun shiga gidan matar ne domin sata, bayan sun kwashe kayanta zasu fita, sai Allah ya sa ta gane daya daga cikinsu, sai ta ce wane har da Kai? Dalilin da ya sanya suka dawo kenan suka bigeta ta fadi sannan suka yanka ta. 
Al’umma da dama suna ganin cewa ‘yan sara suka ne suka rikide zuwa sace-sace domin samun kudin siyen kayayyakin maye.
Tuni dai aka yi jana’izar wannan tsohuwar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

You may also like