An Yi Wa ‘Yan fashi Yankan Rago A Jihar KebbiWasu ‘yan fashi da makami sun hadu da ajalinsu a kauyen Fana dake karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi, bayan sun tare wasu mutane da niyar su karbi kudi a hannunsu, inda mutun daya daga cikin wadanda aka tare ya yi kukan kura ya rungumi daya daga cikin ‘yan fashin dake rike da wuka. Yayin da wani kuma ya rike daya dake rike da bindiga.

Wanda ya rike dan fashi mai rike da wukan ya yi nasarar kwace wukar, inda ya yi wa Dan fashin yankar rago. Shi kuma dayan suka ci gaba da dukan sa saida ya mutu.
‘Yan fashin dai su uku ne, daya ya tsere biyu aka kashe kuma an kawo su babban asibitin dake garin Kamba, inda mutane ke tururuwa don gani da ido.

Karamar hukumar Dandi dai tana daya daga cikin wuraren da ‘yan fashi ke damu inda lokaci zuwa lokaci suna tare mutane. Sannan kuma bincike ya nuna cewa wadannan ‘yan fashi da aka kashe duk Fulani ne.

You may also like