An Yiwa Yara 5000 Maganin Cutar Gubar Dalma A Jihar Zamfara Shugaban kungiyar likitoci masu bada agaji ta MSF (Doctor’s without Borders)  a Najeriya ,Philip Aruna  yace kungiyar tayi nasarar yiwa yara 5000  magani bayan da suka kamu da cuta gubar dalma a Jihar Zamfara, tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu. 

Idan za’a iya tunawa guba dalma na daya daga cikin gubar dake, hallaka yara wanda ta hallaka yara sama 300 tun lokacin da cutar ta bulla. 

 Da yake jawabi yayin bude wani taron masu bada tallafin kan harkokin hakar ma’adanai, da aka gudanar a Abuja,  shugaban yace “Zuwa yanzu kungiyar da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya sunyi nasarar yiwa yara 5000 dake da irin wannan matsala magani a jihar Zamfara”

Mista Aruna yace ” Mun zata irin wannan matsala tazo karshe, muna tsaka da neman hanyar da zamu kare faruwar haka anan gaba, kawai cikin watan Afirilun 2015 sai matsala irin haka ta kara faruwa a jihar Neja, a al’ummar  shikira, inda aka gabatar da yara masu dauke da irin wanna matsalar, kuma an gano cewa hakan na da alaka da yadda ake hakar ma’adanai a gargakiyance”

Yakara da cewa yanzu haka kungiyar na aiki a jihohin Neja da Zamfara domin maganin gubar dalma. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like