An Zabi Antonio Guterres A Matsayin Sabon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. 


A kuri’ar da aka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis, membobin Majalisar sun zabi tsohon Firayi ministan kasar Portugal Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce a jiya Alhamis ne babban zauren ya zabi Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren MDD wanda kuma shi ne zai zama babban sakataren majalisar na tara har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Misata Antonio Guterres dan shekaru 67 a duniya zai maye gurbin babban sakataren majalisar na yanzu Ban Ki Moon dan shekaru 72 a duniya wanda zai sauka daga wannan mukamin a karshen wannan shekara ta  2016 bayan ya yi wa’adi biyu na mulkinsa.
Mista Guterres ya rike mukamin Firayi Ministan Portugal din ne daga shekarar 1995 zuwa 2002 sannan kuma ya rike babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniyan kan lamurran ‘yan gudun hijira daga shekara ta  2005 zuwa 2015.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like