An zargi fulani makiyaya da kashe mutane 24 a wasu sababbin hare-hare a jihar Benue


Akalla mutane 10 aka bada rahoton an kashe a wasu sababbin hare-hare da ake zargin fulani makiyaya ne suka kai a jihar Benue.

Yayan majalisar wakilai ta tarayya da suka fito daga jihar Benue sune suka bayyana haka a ranar Alhamis.

An aiwatar da kisan mutanen tsakanin ranakun 2 da kuma 4 ga watan Afirilu.

Da suke wa yan jaridu jawabi a Abuja, yan majalisar sun yi zargin cewa makiyayan masu kisa sun kai hari kan garuruwa bakwai a jihar ya yin da suka yi wa wasu kuma kawanya.

Dickson Takighir, wanda ya yi magana a madadin abokanan aikinsa ya ce:”wadannan hare-hare na baya-bayannan an kai sune a Ikon a ranar 3 da kuma 4 ga watan Afirilu; a garuruwan Semaka, Asom, Babanruwa, a ranar uku ga watan Afirilu da kuma Udei da Umenger a ranar 2 ga watan Afirilu.

Yan majalisar sun kuma zargin yan sanda da jan kafa wajen aiwatar da dokar hana kiwon dabbobi a fili.

You may also like