
Asalin hoton, ALAMY/REUTERS
Sabon Babban Massallacin na Masar zai iya daukar masallata dubu 107
Masar ta bude wani katafaren masallaci wanda ya kafa tarihi ta fannoni da dama da kuma kasancewa na biyu mafi girma yanzu a Afirka, a sabon babban birnin kasar, sai dai kuma jama’a na ta suka a kan yawan kudin da aka kashe.
Gwamnatin kasar tana gina sabon birnin na mulki ne a cikin hamada, a wani wuri da ke da nisan kilomita 45, gabas da Alkahira, domin rage yawan mutane daga babban birnin na yanzu wanda ya cika ya batse da jama’a.
Sai dai kuma bude sabon masallacin tare da wata babbar cibiyar harkokin Musulunci ta janyo ce-ce-ku-ce da suka daga mutane da dama a shafukan sada zumunta da muhawara.
Jama’a na kokawa da ayyukan kan dimbin kudin da aka kashe yayin da kasar ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka, inda lamarin ya wuce kashi 30 cikin dari a watan Maris din nan.
Sabuwar cibiyar da harkokin Musuluncin wadda ta kunshi wannan katafaren masallaci tana da fadin murabba’in mita 19,000, kuma za ta iya daukar masu ibada dubu 107,000.
An kashe fam din Masar miliyan 800, kwatankwacin dala miliyan 25.9, a ginin massallacin wanda a yanzu shi ne na biyu a girma a Afirka, bayan Djamaa el Djazaïr da ke babban birnin Algeria, Algiers.
Kafar yada labarai ta gwamnatin Masar ta bayyana cewa masallacin ya zama na daya yanzu a fannoni uku a tsakanin masallatai na duniya.
Abu na farko shi ne mumbarinsa shi ne mafi tsawo yanzu a duniya, inda yake da tsawon mita 16.6 wato kafa 54 da rabi, kuma an yi mumbarin ne da wani itace mai kyau sosai
Abu na biyu da kuma na uku da masallacin ya zarta kowanne a duniya kuma shi ne fitilarsa ta rataye da ke tsakiyar kwaryar masallacin irin mai adon nan, ita ce mafi nauyi a duniya, inda ta kai nauyin kilogram 24,300, kuma ita ce mafi girma, da tsawon tsakiyarta ya kai kafa 72.2, sannan tana da hawa hudu.
Shugaban kasar ta Masar Abdul Fattah al-Sisi, ya halarci bikin bude masallacin, wanda kafar yada labaran kasar ta bayyana aikin a matsayin ”Tsabar Gwanintar Masar”.
Yayin a daya bangaren ake ta suka a shafukan sada zumunta da muhawara kan aikin ginin cibiyar da kuma masallacin ganin irin dimbin kudin da aka kashe.
Asalin hoton, Reuters
Sabon Babban Birnin Mulki na Masar yana nisan kilomita 45 gabas da Alkahira
Masar na fama da gagarumar matsalar tattalin arziki, kasancewar kudinta ya rasa kusan rabin darajarsa a kan dala a cikin shekara daya da ta gabata, wanda hakan ya sa hauhawar farashin kaya da ayyuka ta kai kololuwar da ba ta taba kaiwa ba a shekara biyar.
Haka kuma kasar na sayar da kadarorinta ga ‘yan kasuwa masu zuba jari na yankin kasashen tekun Fasha, domin ta samu kudin da za ta cike wagegen gibin kasafin kudinta.
Mutane da dama sun rika sukar hukumomin kasar a shafukan Twitter da Facebook, kan yadda suka ce tana kashe kudi a kan wuraren addini a wannan lokaci mai tsanani da miliyoyin ‘yan Masar ke fama da abin da za su ci.
Wani da ya yi rubutu a Facebook, kan abin da ya bayyana da barnar kudin da gwamnati ta yi a masallacin, cewa ya yi a sayar da fitilar ratayen da kuma mumbarin da ma masallacin gaba daya idan har hakan zai ka iya magance matsalar da ake ciki.
Wani kuma cewa ya yi a rufe masallacin duk tsawon shekara, a rika bude shi duk bayan wata uku, saboda mutane dari daya su yi amfani da shi, sai kuma a sake rufe shi.
Shi kuma wani suka ya yi kan makudan kudaden da gwamnati ke kashewa a manyan ayyuka.
Yana cewa,”to me za mu yi da mutanen da ba su da abin da za su ci ko matasan da ba za su iya aure ba? Ba matsala. Muna da masallaci mafi girma, fitalar kawa ta masallaci wadda ta fi nauyi da kuma bashin waje mafi girma wanda za mu ci gaba da biya har ranar tashin kiyama.”
Shugaba Sisi wanda ya jagoranci sojoji suka hambarar da wanda ya gada Mohammed Morsi, a 2013 sakamakon zang-zanga a kan gwamnatin marigayin ya yaba wa wadanda suka halarci bikin bude masallacin da sauran jama’a a wurin wanda firaministan kasar shi ma ya halarta.
Kakakinsa ya rika sanya hotuna na shugaban a wurin bikin a shafukan intanet, abin da kafafaen yada labarai na kasar suka bayyana da kaddamar da sabuwar jamhuriyya.