Ana ci gaba da barin wuta a Sudan | Labarai | DWRahotanni daga kasar na cewa a jiya Asabar an ci gaba da dauki ba dadi a birnin Khartum da yankin Darfur inda bangarorin habsan sojan biyu suka yi ta kai wa junansu hare-hare ta jiragen sama da kuma mayan bindigogi.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da yadda manyan habsan sojan suka bijirewa kiraye-kirayen tsagaita buda wuta yayin da yakin ya kama hanyar daidaita kasar da dama ba ta dinke ba daga tsohon rikicin Darfur.

Kawo yanzu rikicin da ya barke a ranar 15 ga watan Aprilu ya yi ajalin mutane sama da 500 tare da jikkatar wasu gwammai baya ga tilasta wa fararen hula sama da dubu 75 gudu daga kasar izuwa kasashen Tchadi, Masar, Habasha da kuma Sudan ta Kudu yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kwashe mutanensu.

A jiya Asabar shugaban Suban ta Kudu Salvakir wanda a can baya ya taka muhinmiyar rawa wajen daidaituwar lamura a Sudan din lokacin barkewar yakin Darfur ya kira manyan habsan sojan da ke kokowar iko da su yi ganawar keke da keke don dinke barakar da ta kunno kai a tsakaninsu ba tare da wata-wata ba. 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like