Ikirarin Shugaba Buhari na kiran matasan Nijeriya ci-ma zaune ya yi matukar harzuka al’ummar Nijeriya da manyan ‘yan siyasa inda ake ci gaba da caccake shugaban inda har wasu ke ganin Shugaban da ‘ya’yansa ne ma ya kamata a a kira ci-ma zaune.
A nasa ra’ayin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai taba kiran matasan Nijeriya ci-ma zaune ba a maimakon haka shi ya san matasan hazikai ne saboda akwai daruruwansu da ke aiki a kamfanoninsa kuma su ne ginshikin bunkasar kasar nan.
Shi kuwa dan majalisar Dattawa daga jihar Bayelsa, Sanata Ben Murray-Bruce cewa ya yi, duk wanda ya kira matasan Nijeriya ci-ma zaune, kamata ya yi ya kalli kansa a cikin madubi wanda daga nan ne zai fahinci ma’anar ci- ma zaune inda ya ce akwai kusan dubu guda da ke aiki karkashinsa.
A bangarensu, matasan jam’iyyar PDP sun yi Allah-wadai da ikirarin Shugaban wanda suka bayyana shi a matsayin annoba wadda suke fatan al’ummar Nijeriya ta rabu da ita.
A jiya ne dai a wurin wani taron kasuwanci na shugabannin kasashen renon Ingila Shugaba Buhari ya ce mafi yawan matasan Nijeriya ba su zuwa Makaranta amma kuma suna son komai arha saboda suna ganin Nijeriya tana da arzikin man fetur.