Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan | Labarai | DWYarjejeniyar da a yau ta shiga rana ta uku ana ci gaba da jiwo amon harbe-harbe a sararin samaniyar kasar.

Da ma dai an cimma tsagaita wutar ne domin bada kofar kai agajin gagawa ga mabukata da har yanzu ke makale a cikin kasar.

Wannan shi ne karo na 4 da ake cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wanda kamar sauran ta baya ba a mutunta ta ba.

Tun a tsakiyar watan Afirilu rikicin shugabanci ya barke a tsakanin sojojin gwamnati karkashin Janar Abdel fatah al-Burhan da na dakarun sa kai na RSF da Mohammaed Hamdan Daglo ke jagoranta.

Janar Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da tsige madugun ‘yan tawayen na RSF Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin mataimakinsa.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like