Ana ci gaba da kai hare-haren tsaron yankin Fırat a arewacin Siriya wanda aka fara kai wa a ranar 24 ga watan Agusta inda ake kokarin korar ‘yan ta’adda daga iyakokin Turkiyya da Siriya.
A ranar Lahadin nan an kai hare-hare ta sama sau 21 kan ‘yan ta’addar Daesh, PYD da PKK.
An jefa bama-bamai 17 kan ‘yan ta’addar Daesh a yankunan arewaci, arewa mas-gabas da yammacin Al-Bab da kuma garuruwan Kabbasin da Suflaniyya.
A hare-haren da jiragen saman Turkiyya suka kai sun sam,i nasarar fasa wasu bama-baman ‘yan ta’addar.
A yankunan Yılanlı da Kurtviran kuma an kai hari sau 4 kan ‘yan ta’addar PYD/PKK.