Ana Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Zaben Trump A Jihohi Daban Daban A Kasar Amurka.


 

4bkbdb24766a2chd37_800c450

Kwanaki ukku a gere masu zanga zanga a birane daban daban a kasar Amurka sun ci ga da yin Al..wadai da sakamakon zaben.

Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran daga Amurkan ta bayyana cewa dubban mutane sun ci gaba da fitowa kan tituna a biranen Miyami, Atlanta, Filadelpia ,New York da kuma Sanfransisco kwanaki ukku a jere suna aibata zabebben shugaban kan ra’yoyinsa kan bakin haure Musulmi da kuma da kuma mata.

A birnin New York daruruwan masu zanga zanga sun sun yi dafifiĀ a dandanlin “Washington Square inda kusa da dogon gini na Donal Trump a birnin sun rare wakokin nuna rashin amincewa da shi.

Tun bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a ranar Laraban da ta gabata masu nuna amincewa da zaben Trump suke fitowa kan tituna suna Al..wadai da sakamakon zaben.

Zabebben shugaban kasar dai ya bayyana a jiya jumma kan cewa wadanda suke bayyana adawa da zabensa sun tasirantu ne da farfagandar kafafen yada labarai.

A ranar 8 ga watan Nuwamba da muke cikine aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Amurka wanda sakamakon ya nuna cewa Donal Trump na Jam’iyar Republican ne ya lashe shi, tare da kada abokiyar hamayarsa Hillary Clinton na jam’iyyar Democrate.

You may also like