Dubunnan Turkawa dake kasashen waje ne suka hau kan tiituna don yin Allah wadai da juyin mulki.
A birnin Toronto na kasar Kanada Turkawa sama da dubu 10 ne suka farwa tituna da taken ”bama son juyin mulki” inda a Paris babban birnin Faransa kuma wasu Turkawa suka isa gurin yawon bude ido hatsumiyar Eiffel Tower tare da rike da tutar kasar don nunawa duniya cewa basu amince da juyin mulki ba.Sun yi taken kasar Turkiyya ne da wasu wake wake kamar haka: ”Al’ummarmu basu mutuwa”, ”shahidun basu mutuwa” ”a kashe maharan” ”kisa muke kauna” kungiyar ta FETO su saurari” Bama son juyin mulki, ”ba zamu yarda da juyin mulki ya fitar da gwamnati da muka zabi ba” ”Zamu rinka kare Demokuradiya”.
Haka kuma a babban birnin Uskup na Macedoniya an gudanar da babbar zanga zangar nuna rashin amincewa da FETO inda suka yi taken cewa ”kar wata kasa ta nunawa Turkawa abinda suke kauna’. A gefe guda kuma wasu sun fara ikirarin da gwamnati ta rufe makarantun Fethulah dake kasar. Sun ce ba zasu yarda ‘ya’yansu su je wannan makarantar FETO ba, sun yi kuskure da farko don haka ba zasu maimaita yin hakan ba.
A birnin Erbil na Iraki al’ummar Turkmen sun nuna nasu goyon bayan gwamnatin Turkiyya inda suka yi Allah wadai da naka ya lalace. Wakilin Erbil a majalisar Dokokin kasar Aydin Maruf ya bada sanarwar goyon bayan Turkiyya da gudanar da zanga zangar kare demokuradiya.