Al’ummar Najeriya mazauna ƙasar Afrika ta Kudu sun ce mutane huɗu yan Najeriya na can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali yayin da aka kona wasu shaguna a wani sabon hari da yan kasar ta Afirka suka kaiwa yan Najeriya.
Paul Nwanedo, shugaban kungiyar yan Najeriya mazauna ƙasar reshen Lardin Arewa maso Yamma ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa harin kan yan Najeriya ya fara ne ranar Lahadi.
Yace direbobin tasi dake garin Rustenburg sun yi zargin cewa wani dan Najeriya ya sace wata yar kasar mai shekaru 16 inda yayi mata fyade kana suka yi ikirarin cewa yan Najeriya na sayarwa da yan daban da suke addabarsu miyagun kwayoyi.
“Wannan karya ce tsagwaronta, mun yi bincike muka kuma gano dukkanin zarge-zargen karyane,kungiyar ta damu da lafiyar ƴaƴanta dake zaune a Rustenburg,” yace.
Nwanedo yace yan Najeriya huɗu da masu tasi ɗin suka kama sun sha dukan tsiya suna can asibiti cikin wani mawuyacin hali yayin da aka kona wasu shaguna mallakin yan Najeriya.
” A yanzu da nake magana da kai a tsorace nake saboda harin ya cigaba, mambobin mu har yanzu na cikin buya.
“Mun kaiwa yan’sanda rahoto da kuma uwar kungiyar mu ta ƙasa.Muna so a kare rayuka da kuma dukiyar mutanen mu.”