Ana Cigaba Da Kashe  Fulani A Yankin Mambila Dake Jihar Taraba 


Sanatan dake wakiltar mazabar Taraba ta tsakiya a majalisar dattawa, Yusuf Abubakar  Yusuf, yace mutane da dama aka kashe, garuruwan Fulani 50 aka kona yayin da akalla shanu 20,000 suka mutu a rikicin da ya barke a yankin Mambila dake jihar Taraba. 

 Da yake magana da jaridar Daily Nigerian a ranar Alhamis, yace wasu mayakan sakai da suka fito da ga wata kabila sune suke kai hari kan matsugunan Fulani dake yankin . 

Sanatan yace koda a yau da safe an samu kai hari akan matsugunan da suke Hayin Kogi.

  ” Yanzu dai an kare manyan garuruwa daga maharan amma suna cigaba da kai harin a wasu kananan kauyuka, ko yau da safen nan an samu kai hari a Hayin Kogi,” yace. 

 Yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tura sojoji zuwa yankin domin kawo karshen hare-haren.

Ana dai zargin kabilun dake yankin na Mambila tare da yan kabilar Jukun da kai harin, wanda ake dangantashi da kisan kare dangi kan Fulanin dake yankin. 

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa mai suna Bello Haruna, yace maharan sun kona dukkanin gidajen dake kauyen,tare da kashe shanun dake garin, inda yace da kyar ya samu ya tsira tare da matarsa da kuma yayansa biyu. 

Al’ummar Fulani dake karamar hukumar Sardauna a jihar ta Taraba sun yi kira ga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da ya kawo karshen abinda suka kira kisan kiyashin da ake musu. 

  Fulanin suna zargin shugaban karamar Hukumar John Yep  da tunzura matasan wajen aikata kisan kare dangin. 

A cewar kakakin rundunar yansandan jihar David Misal rikicin ya samo asaline bayan da wata kotu a garin Gembu ta bada umarni da a tsare wani dan asalin kabilar yankin Mambila sakamakon karar da wani bafulatani yakaishi. 

 ” Yayan dan kabilar yankin sunje gidan mutumin  da yakai karar wanda dan Fulani ne mai suna Riwi Ahmadu inda suka bukaci da ya sa a  sako babansu ko kuma suyi maganinsa. 

” Bayan da yaki aiwatar da abinda suka nema sai suka gonawa mai karar gida, tare da ji masa rauni, ” Misal yace. 

 Yace yan sanda sun shiga tsakani inda suka kama wadanda suka konawa Ahmadu gidansa.  

You may also like