Ana Cigaba Da Kashe Mutane A Rikicin Kan Iyaka A jihohin Cross River Da Ebonyi A kalla mutane 9 aka kashe da suka hada da wata mace mai ciki  a wani sabon rikicin kan iyaka tsakanin al’umomin Ofioji a karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi da kuma na Ijutun-Idoru dake karamar hukumar Obubura dake jihar Cross River a cewar mazauna yankin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Jude Madu,  ya tabbatar da barkewar rikicin a yankin amma yace rundunar har yanzu bata tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba. 

” Mun tura jami’an tsaro domin dakatar da harin a kwanaki masu zuwa zamu tabbatar da abinda yafaru ko akwai wadanda suka rasa rayukansu,” Madu yace. 

 Wasu maigidanta sun ce mutanen Ijutun-Idoru dake jihar Cross River sune suka mamaye Ofioji da safiyar ranar juma’a suna harbin kan me uwa da wabi inda suka kashe mutane 9.

Shugaban al’ummar yankin na Ofioji yayi cikakken bayani kan yadda harin yafaru inda yace yana magana ne daga wani wuri da yake boye yayi kira ga gwamnatin jiha da kuma ta tarayya kan su kawo musu dauki.

Mista Mbam yace wata mata mai ciki da ya bayyana da suna Ukamaka Nwifuru, na daga cikin wadanda aka kashe a harin.

“Da daren ranar juma’a duk mun tafi gida muna cikin bacci, kawai sai mukaji wata kara a garin inda muka firgita mukayi waje kawai sai muka ga gidaje da yawa suna cin wuta sannan ne muka gano cewa mutanen Cross River ne suka kawo mana hari suna harbin mutanen mu babu tausayi sun kona gidajen mu kana suka debe mana dukiya,” yace. 

Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya bayyana harin a matsayin wani abu na rashin kan gado. kana yayi kira ga babban hafsan sojin Kasan Najeriya Tukur Yusuf Buratai kan ya tura jami’an soji domin kawo karshen hare-haren.

You may also like