Ana Cigaba Da Nuna Alhinin Mutuwar Lil Ameer 


Jama’a da dama na cigaba da nuna alhininsu da kuma mika ta’aziyarsu ga iyalan mawakin nan  Ameer Isa Hassan wanda akafi sani da Lil Ameer. 

Dan autan mawakan Hausa Hip Hop kamar yadda wasu suke kiransa ya rasa ransa bayan da wata mota ta babur din da yake kai.

Tuni dai aka binne shi a yau Juma’a kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Ameer ya fara waka tun yana dan shekara 12,tun daga wannan lokaci yayi wakoki dama da suka hada da “Kai Matsa Mana, Dance For Me,  I am A Champion, da sauransu.

A sakon da ya rubuta a shafinsa na Facebook, Adam A Zango yace ya kadu matukar kaduwarsa da mutuwar mawakin.  

Sauran yan wasan Hausa da mawaka duk sun nuna jimaminsu da mutuwar Lil Ameer. 

Mawakin ya rasu yana da shekara 14 a duniya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like